نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
159 | 2 | 152 | فاذكروني أذكركم واشكروا لي ولا تكفرون |
| | | Sabõda haka, ku tuna Ni, In tunã ku, kuma ku yi gõdiya gare Ni, kuma kada ku butulce Mini. |
|
160 | 2 | 153 | يا أيها الذين آمنوا استعينوا بالصبر والصلاة إن الله مع الصابرين |
| | | Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nẽmi taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tãre da mãsu haƙuri. |
|
161 | 2 | 154 | ولا تقولوا لمن يقتل في سبيل الله أموات بل أحياء ولكن لا تشعرون |
| | | Kada ku ce ga waɗanda ake kashẽwa a cikin hanyar Allah: "Matattu ne." Ã'a, rãyayyu ne, kuma amma bã ku sansancẽwa. |
|
162 | 2 | 155 | ولنبلونكم بشيء من الخوف والجوع ونقص من الأموال والأنفس والثمرات وبشر الصابرين |
| | | Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙasa daga dũkiya da rãyuka da 'ya'yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri. |
|
163 | 2 | 156 | الذين إذا أصابتهم مصيبة قالوا إنا لله وإنا إليه راجعون |
| | | Waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmãwa." |
|
164 | 2 | 157 | أولئك عليهم صلوات من ربهم ورحمة وأولئك هم المهتدون |
| | | Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan sũ ne shiryayyu. |
|
165 | 2 | 158 | إن الصفا والمروة من شعائر الله فمن حج البيت أو اعتمر فلا جناح عليه أن يطوف بهما ومن تطوع خيرا فإن الله شاكر عليم |
| | | Lalle ne Safã da Marwa suna daga wurãren ibãdar Allah, to, wanda ya yi hajin ¦ãki kõ kuwa ya yi Umra, to, bãbu laifi a kansa ga ya yi ɗawãfi gare su, su biyu. Kuma wanda ya ƙãra yin wani aikin alhẽri to, lalle ne Allah Mai gõdiya ne, Masani. |
|
166 | 2 | 159 | إن الذين يكتمون ما أنزلنا من البينات والهدى من بعد ما بيناه للناس في الكتاب أولئك يلعنهم الله ويلعنهم اللاعنون |
| | | Lalle ne waɗanda suke ɓõyẽwar abin da Allah Ya saukar da ga hujjõji bayyanannu, da shiriya, daga bãyan Mun bayyana shi ga mutãne, a cikin Littãfi (Alƙur'ãni), waɗannan Allah Yana la'anar su, kuma mãsu la'ana suna la'anar su. |
|
167 | 2 | 160 | إلا الذين تابوا وأصلحوا وبينوا فأولئك أتوب عليهم وأنا التواب الرحيم |
| | | Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka bayyana, to waɗannan Ina karɓar tũba a kansu kuma Nĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai. |
|
168 | 2 | 161 | إن الذين كفروا وماتوا وهم كفار أولئك عليهم لعنة الله والملائكة والناس أجمعين |
| | | Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai, waɗannan akwai, a kansu, la'anar Allah da Malã'iku da mutãne gabã ɗaya. |
|