نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1573 | 11 | 100 | ذلك من أنباء القرى نقصه عليك منها قائم وحصيد |
| | | Wancan Yanã daga lãbãran alƙaryõyi. Munã bã ka lãbãrinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe. |
|
1574 | 11 | 101 | وما ظلمناهم ولكن ظلموا أنفسهم فما أغنت عنهم آلهتهم التي يدعون من دون الله من شيء لما جاء أمر ربك وما زادوهم غير تتبيب |
| | | Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun zãlunci kansu sa'an nan abũbuwan bautawarsu waɗanda suke kiran su, baicin Allah, ba su wadãtar musu kõme ba a lõkacin da umurnin Ubangijinka ya je, kuma (gumãkan) ba su ƙãra musu wani abu ba fãce hasãra. |
|
1575 | 11 | 102 | وكذلك أخذ ربك إذا أخذ القرى وهي ظالمة إن أخذه أليم شديد |
| | | Kuma kamar wancan ne kãmun Ubangijinka, idan Ya kãma alƙaryõyi alhãli kuwa sunã mãsu zãlunci. Lalle kamũnSa mai raɗaɗi ne, mai tsanani. |
|
1576 | 11 | 103 | إن في ذلك لآية لمن خاف عذاب الآخرة ذلك يوم مجموع له الناس وذلك يوم مشهود |
| | | Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga wanda ya ji tsõron azãbar Lãhira. Wancan yini ne wanda ake tãra mutãne a cikinsa kuma wancan yini ne abin halarta. |
|
1577 | 11 | 104 | وما نؤخره إلا لأجل معدود |
| | | Ba Mu jinkirtã shi ba fãce dõmin ajali ƙidãyayye. |
|
1578 | 11 | 105 | يوم يأت لا تكلم نفس إلا بإذنه فمنهم شقي وسعيد |
| | | Rãnar da za ta zo wani rai ba ya iya magana fãce da izninSa. Sa'an nan daga cikinsu akwai shaƙiyyi da mai arziki. |
|
1579 | 11 | 106 | فأما الذين شقوا ففي النار لهم فيها زفير وشهيق |
| | | To, amma waɗanda suka yi shaƙãwa, to, sunã a cikin wuta. Sunã mãsu ƙãra da shẽka acikinta. |
|
1580 | 11 | 107 | خالدين فيها ما دامت السماوات والأرض إلا ما شاء ربك إن ربك فعال لما يريد |
| | | Suna madawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Lalle Ubangijinka Mai aikatãwa ne ga abin da Yake nufi. |
|
1581 | 11 | 108 | وأما الذين سعدوا ففي الجنة خالدين فيها ما دامت السماوات والأرض إلا ما شاء ربك عطاء غير مجذوذ |
| | | Amma waɗanda suka yi arziki to, sunã a cikin Aljanna sunã madawwama, a cikinta, matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Kyauta wadda bã ta yankẽwa. |
|
1582 | 11 | 109 | فلا تك في مرية مما يعبد هؤلاء ما يعبدون إلا كما يعبد آباؤهم من قبل وإنا لموفوهم نصيبهم غير منقوص |
| | | Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da waɗannan suke bautawa. Bã su wata ibãda fãce kamar yadda ubanninsu ke aikatãwa a gabani. Kuma haƙĩƙa Mũ, Mãsu cika musu rabon su ne, bã tãre da nakasãwa ba. |
|