نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1533 | 11 | 60 | وأتبعوا في هذه الدنيا لعنة ويوم القيامة ألا إن عادا كفروا ربهم ألا بعدا لعاد قوم هود |
| | | Kuma an biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. To! Lalle ne Ãdãwa sun kãfirta da Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Ãdãwa, mutãnen Hũdu! |
|
1534 | 11 | 61 | وإلى ثمود أخاهم صالحا قال يا قوم اعبدوا الله ما لكم من إله غيره هو أنشأكم من الأرض واستعمركم فيها فاستغفروه ثم توبوا إليه إن ربي قريب مجيب |
| | | Kuma zuwa ga Samũdãwa (an aika) ɗan'uwansu Sãlihu. Ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Shĩ ne Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma Ya sanya ku mãsu yin kyarkyara a cikinta. Sai ku nẽme Shi gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai karɓãwa." |
|
1535 | 11 | 62 | قالوا يا صالح قد كنت فينا مرجوا قبل هذا أتنهانا أن نعبد ما يعبد آباؤنا وإننا لفي شك مما تدعونا إليه مريب |
| | | Suka ce: "Ya Sãlihu! Haƙĩƙa, kã kasance a cikinmu, wanda ake fatan wani alhẽri da shi a gabãnin wannan. Shin kana hana mu bauta wa abin da ubanninmu suke bauta wa? Kuma haƙĩƙa mũ, munã cikin shakka daga abin da kake kiran mu gare shi, mai sanya kõkanto." |
|
1536 | 11 | 63 | قال يا قوم أرأيتم إن كنت على بينة من ربي وآتاني منه رحمة فمن ينصرني من الله إن عصيته فما تزيدونني غير تخسير |
| | | Ya ce: "Ya mutãnẽna! Kun gani? Idan na kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Ya bã ni rahama daga gare Shi, to, wane ne zai taimake ni daga Allah idan nã sãɓa Masa? Sa'an nan bã zã ku ƙãre ni da kõme ba fãce hasãra." |
|
1537 | 11 | 64 | ويا قوم هذه ناقة الله لكم آية فذروها تأكل في أرض الله ولا تمسوها بسوء فيأخذكم عذاب قريب |
| | | "Kuma ya mutãnena! wannan rãƙumar Allah ce, tanã ãyã a gare ku. Sai ku bar ta ta ci a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta kar azãba makusanciya ta kãma ku." |
|
1538 | 11 | 65 | فعقروها فقال تمتعوا في داركم ثلاثة أيام ذلك وعد غير مكذوب |
| | | Sai suka sõke ta. Sai ya ce: "Kuji dãɗi a cikin gidãjenku kwãna uku. Wannan wa'adi ne bã abin ƙaryatãwa ba." |
|
1539 | 11 | 66 | فلما جاء أمرنا نجينا صالحا والذين آمنوا معه برحمة منا ومن خزي يومئذ إن ربك هو القوي العزيز |
| | | To, a lõkacin da umurninMu ya je, muka kuɓutar da Sãlihu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma daga wulãkancin rãnar nan. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMai ƙarfi, Mabuwãyi. |
|
1540 | 11 | 67 | وأخذ الذين ظلموا الصيحة فأصبحوا في ديارهم جاثمين |
| | | Sai tsãwa ta kãma waɗanda suka yi zãlunci, sai suka wãyi gari sunã guggurfãne a cikin gidãjensu. |
|
1541 | 11 | 68 | كأن لم يغنوا فيها ألا إن ثمود كفروا ربهم ألا بعدا لثمود |
| | | Kamar dai ba su zauna a cikinta ba. To! Lalle ne samũdãwa sun kãfirce wa Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Samũdãwa. |
|
1542 | 11 | 69 | ولقد جاءت رسلنا إبراهيم بالبشرى قالوا سلاما قال سلام فما لبث أن جاء بعجل حنيذ |
| | | Kuma haƙĩƙa, manzanninMu sun je wa Ibrãhim da bushãra suka ce: "Aminci." Ya ce: "Aminci (ya tabbata a gare ku)." Sa'an nan bai yi jinkiri ba ya je da maraƙi ƙawãtacce. |
|