نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1516 | 11 | 43 | قال سآوي إلى جبل يعصمني من الماء قال لا عاصم اليوم من أمر الله إلا من رحم وحال بينهما الموج فكان من المغرقين |
| | | Ya ce: "Zan tattara zuwa ga wani dũtse ya tsare ni daga ruwan." (Nũhu) ya ce: "Bãbu mai tsarẽwa a yau daga umurnin Allah fãce wanda Ya yi wa rahama." Sai taguwar ruwa ta shãmakace a tsakãninsu, sai ya kasance daga waɗanda aka nutsar. |
|
1517 | 11 | 44 | وقيل يا أرض ابلعي ماءك ويا سماء أقلعي وغيض الماء وقضي الأمر واستوت على الجودي وقيل بعدا للقوم الظالمين |
| | | Kuma aka ce: "Yã ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yã sama! Ki kãme."Kuma aka faƙar da ruwan kuma aka hukunta al'amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi, kuma aka ce: "Nĩsa ya tabbata ga mutãne azzãlumai." |
|
1518 | 11 | 45 | ونادى نوح ربه فقال رب إن ابني من أهلي وإن وعدك الحق وأنت أحكم الحاكمين |
| | | Kuma Nũhu ya kira Ubangijinsa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne ɗãna na daga iyãlĩna! Kuma haƙĩƙa wa'adinKa gaskiya ne, kuma Kai ne Mafi hukuncin mãsu yin hukunci." |
|
1519 | 11 | 46 | قال يا نوح إنه ليس من أهلك إنه عمل غير صالح فلا تسألن ما ليس لك به علم إني أعظك أن تكون من الجاهلين |
| | | Ya ce: "Yã Nũhu! Lalle ne shi bã ya a ciki iyãlanka, lalle ne shĩ, aiki ne wanda ba na ƙwarai ba, sabõda haka kada ka tambaye Ni abin da bã ka da ilmi a kansa. Haƙĩƙa, Nĩ Inã yi maka gargaɗi kada ka kasance daga jãhilai." |
|
1520 | 11 | 47 | قال رب إني أعوذ بك أن أسألك ما ليس لي به علم وإلا تغفر لي وترحمني أكن من الخاسرين |
| | | Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, inã nẽman tsari gare Ka da in tambaye Ka abin da bã ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka gãfarta mini ba, kuma Ka yi mini rahama, zan kasance daga mãsu hasãra." |
|
1521 | 11 | 48 | قيل يا نوح اهبط بسلام منا وبركات عليك وعلى أمم ممن معك وأمم سنمتعهم ثم يمسهم منا عذاب أليم |
| | | Aka ce: "Ya Nũhu! Ka sauka da aminci da, a gare Mu da albarka a kanka, kuma rahama ta tabbata a kan waɗansu al'ummõmi daga waɗanda suke tãre da kai. Da waɗansu al'ummõmi da zã Mu jiyar da su dãɗi, sa'an nan kuma azãba mai raɗaɗi ta shafe su daga gare Mu." |
|
1522 | 11 | 49 | تلك من أنباء الغيب نوحيها إليك ما كنت تعلمها أنت ولا قومك من قبل هذا فاصبر إن العاقبة للمتقين |
| | | Waccan ƙissa tanã daga lãbãran gaibi, Munã yin wahayinsu zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance kanã sanin su ba, haka kuma mutãnenka ba su sani ba daga gabãnin wannan. Sai ka yi haƙuri. Lalle ne ãƙiba tanã ga mãsu taƙawa, |
|
1523 | 11 | 50 | وإلى عاد أخاهم هودا قال يا قوم اعبدوا الله ما لكم من إله غيره إن أنتم إلا مفترون |
| | | Kuma zuwa ga Ãdãwa, (Mun aika) ɗan'uwansu Hũdu. Ya ce: "Yã kũ mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Ba ku kasance ba fãce kunã mãsu ƙirƙirãwa. |
|
1524 | 11 | 51 | يا قوم لا أسألكم عليه أجرا إن أجري إلا على الذي فطرني أفلا تعقلون |
| | | "Yã ku mutãnena! Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce ga wanda Ya ƙãga halittata. Shin fa, bã ku hankalta?" |
|
1525 | 11 | 52 | ويا قوم استغفروا ربكم ثم توبوا إليه يرسل السماء عليكم مدرارا ويزدكم قوة إلى قوتكم ولا تتولوا مجرمين |
| | | "Kuma, ya mutãnena! Ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi, zai saki sama a kanku, tanã mai yawan zubar da ruwa, kuma Ya ƙãra muku wani ƙarfi ga ƙarfinku. Kuma kada ku jũya kunã mãsu laifi." |
|