نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1505 | 11 | 32 | قالوا يا نوح قد جادلتنا فأكثرت جدالنا فأتنا بما تعدنا إن كنت من الصادقين |
| | | Suka ce: "Yã Nũhu, lalle ne kã yi jayayya da mu, sa'an nan kã yawaita yi mana jidãli, to, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi idan kã kasance daga mãsu gaskiya." |
|
1506 | 11 | 33 | قال إنما يأتيكم به الله إن شاء وما أنتم بمعجزين |
| | | Ya ce: "Allah kawai ne Yake zo muku da shi idan Ya so. Kuma ba ku zama mabuwãya ba." |
|
1507 | 11 | 34 | ولا ينفعكم نصحي إن أردت أن أنصح لكم إن كان الله يريد أن يغويكم هو ربكم وإليه ترجعون |
| | | "Kuma nasĩhãta bã zã ta amfãne ku ba, idan nã yi nufin in yi muku nasĩha, idan Allah Yakasance Yanã nufin Ya halaka ku. Shĩ ne Ubangijinku, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku." |
|
1508 | 11 | 35 | أم يقولون افتراه قل إن افتريته فعلي إجرامي وأنا بريء مما تجرمون |
| | | Ko sunã cẽwa: (Nũhu) ya ƙirƙira shi. Ka ce: "Idan nĩ (Nũhu) na ƙirƙira shi to, laifĩnã a kaina yake, kuma nĩ mai barrantã ne daga abin da kuke yi na laifi." |
|
1509 | 11 | 36 | وأوحي إلى نوح أنه لن يؤمن من قومك إلا من قد آمن فلا تبتئس بما كانوا يفعلون |
| | | Kuma aka yi wahayi zuwa ga Nũhu cẽwa: Lalle ne bãbu mai yin ĩmãni daga mutãnenka fãce wanda ya riga ya yi ĩmãnin, sabõdahaka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa. |
|
1510 | 11 | 37 | واصنع الفلك بأعيننا ووحينا ولا تخاطبني في الذين ظلموا إنهم مغرقون |
| | | Kuma ka sassaƙa jirgi da kyau a kan idanunMu da wahayinMu, kuma kada ka yi Mini magana a cikin sha'anin waɗanda suka kãfirta, lalle ne sũ, waɗanda akenutsarwa ne. |
|
1511 | 11 | 38 | ويصنع الفلك وكلما مر عليه ملأ من قومه سخروا منه قال إن تسخروا منا فإنا نسخر منكم كما تسخرون |
| | | Kuma Yanã sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kõ yaushe waɗansu shugabanni daga mutãnensa suka shũɗe a gabansa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: "Idan kun yi izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mã zã mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin izgili. |
|
1512 | 11 | 39 | فسوف تعلمون من يأتيه عذاب يخزيه ويحل عليه عذاب مقيم |
| | | "Sa'an nan da sannu zã ku san wanda azãba zã ta zo masa, ta wulakantã shi (a dũniya), kuma wata azãba zaunanna ta sauka a kansa (a Lãhira)." |
|
1513 | 11 | 40 | حتى إذا جاء أمرنا وفار التنور قلنا احمل فيها من كل زوجين اثنين وأهلك إلا من سبق عليه القول ومن آمن وما آمن معه إلا قليل |
| | | Har a lõkacin da umurninMu ya je, kuma tandã ta ɓulɓula. Muka ce: "Ka ɗauka, a cikinta, daga kõme, ma'aura biyu, da kuma iyalanka, fãce wanda magana ta gabãta a kansa, da wanda ya yi ĩmãni." Amma kuma bãbu waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi fãce kaɗan." |
|
1514 | 11 | 41 | وقال اركبوا فيها بسم الله مجراها ومرساها إن ربي لغفور رحيم |
| | | Kuma ya ce: "Ku hau a cikinta, da sũnan Allah magudãnarta da matabbatarta. Lalle ne Ubangijĩna, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." |
|