نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1499 | 11 | 26 | أن لا تعبدوا إلا الله إني أخاف عليكم عذاب يوم أليم |
| | | "Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ, inã jin tsõron azãbar yini mai raɗaɗi a kanku." |
|
1500 | 11 | 27 | فقال الملأ الذين كفروا من قومه ما نراك إلا بشرا مثلنا وما نراك اتبعك إلا الذين هم أراذلنا بادي الرأي وما نرى لكم علينا من فضل بل نظنكم كاذبين |
| | | Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta, daga mutãnensa, suka ce: "Bã mu ganin ka fãce mutum kake kamarmu, kuma ba mu ganin wani ya bĩ ka fãce waɗanda suke sũ ƙasƙantattunmu ne marasa tunani. Kuma bã mu ganin wata falalã agare ka a kanmu. Ã'a, Munã zaton ku maƙaryata ne." |
|
1501 | 11 | 28 | قال يا قوم أرأيتم إن كنت على بينة من ربي وآتاني رحمة من عنده فعميت عليكم أنلزمكموها وأنتم لها كارهون |
| | | Ya ce: "Ya mutãnena! Shin, kun gani idan na kasance a kan wata hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Yã bã ni wata Rahama daga wurinSa, Sa'an nan aka rufe ta (ita Rahamar) daga gare ku, shin, zã mu tĩlasta mukuita, alhãli kuwa kũ mãsu ƙi gare ta ne? |
|
1502 | 11 | 29 | ويا قوم لا أسألكم عليه مالا إن أجري إلا على الله وما أنا بطارد الذين آمنوا إنهم ملاقو ربهم ولكني أراكم قوما تجهلون |
| | | "Kuma yã mutãnena! Bã zan tambaye ku wata dũkiya ba akansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce daga Allah, kuma ban zama mai kõrar waɗanda suka yĩ ĩmãni ba. Haƙĩƙa sũ, mãsu haɗuwa da Ubangijinsu ne, kuma amma ni, inã ganin ku mutãne ne jãhilai." |
|
1503 | 11 | 30 | ويا قوم من ينصرني من الله إن طردتهم أفلا تذكرون |
| | | "Kuma ya mutãnena! Wãne ne yake taimakõna daga Allah idan na kõre su? Ashe, bã ku tunãni?" |
|
1504 | 11 | 31 | ولا أقول لكم عندي خزائن الله ولا أعلم الغيب ولا أقول إني ملك ولا أقول للذين تزدري أعينكم لن يؤتيهم الله خيرا الله أعلم بما في أنفسهم إني إذا لمن الظالمين |
| | | "Kuma bã ni ce muku a wurĩna taskõkin Allah suke kuma bã inã sanin gaibi ba ne. Kuma ba inã cẽwa ni Malã'ika ba ne. Kuma ba ni cẽwa ga waɗanda idãnunku suke wulãkantãwa, Allah bã zai bã su alhẽri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (nã yi haka) dã ina daga cikin azzalumai." |
|
1505 | 11 | 32 | قالوا يا نوح قد جادلتنا فأكثرت جدالنا فأتنا بما تعدنا إن كنت من الصادقين |
| | | Suka ce: "Yã Nũhu, lalle ne kã yi jayayya da mu, sa'an nan kã yawaita yi mana jidãli, to, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi idan kã kasance daga mãsu gaskiya." |
|
1506 | 11 | 33 | قال إنما يأتيكم به الله إن شاء وما أنتم بمعجزين |
| | | Ya ce: "Allah kawai ne Yake zo muku da shi idan Ya so. Kuma ba ku zama mabuwãya ba." |
|
1507 | 11 | 34 | ولا ينفعكم نصحي إن أردت أن أنصح لكم إن كان الله يريد أن يغويكم هو ربكم وإليه ترجعون |
| | | "Kuma nasĩhãta bã zã ta amfãne ku ba, idan nã yi nufin in yi muku nasĩha, idan Allah Yakasance Yanã nufin Ya halaka ku. Shĩ ne Ubangijinku, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku." |
|
1508 | 11 | 35 | أم يقولون افتراه قل إن افتريته فعلي إجرامي وأنا بريء مما تجرمون |
| | | Ko sunã cẽwa: (Nũhu) ya ƙirƙira shi. Ka ce: "Idan nĩ (Nũhu) na ƙirƙira shi to, laifĩnã a kaina yake, kuma nĩ mai barrantã ne daga abin da kuke yi na laifi." |
|