نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1469 | 10 | 105 | وأن أقم وجهك للدين حنيفا ولا تكونن من المشركين |
| | | "Kuma (an ce mini): Ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga mãsu shirka. |
|
1470 | 10 | 106 | ولا تدع من دون الله ما لا ينفعك ولا يضرك فإن فعلت فإنك إذا من الظالمين |
| | | "Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci." |
|
1471 | 10 | 107 | وإن يمسسك الله بضر فلا كاشف له إلا هو وإن يردك بخير فلا راد لفضله يصيب به من يشاء من عباده وهو الغفور الرحيم |
| | | Kuma idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, bãbu mai yãyẽ ta fãce shi, kuma idan Yanã nufin ka da wani alhẽri, to, bãbumai mayar da falalarSa. Yanã sãmun wanda Yake so daga cikin bãyinSa da shi. Kuma Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. |
|
1472 | 10 | 108 | قل يا أيها الناس قد جاءكم الحق من ربكم فمن اهتدى فإنما يهتدي لنفسه ومن ضل فإنما يضل عليها وما أنا عليكم بوكيل |
| | | Ka ce: "Yã ku mutãne! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakĩli a kanku ba." |
|
1473 | 10 | 109 | واتبع ما يوحى إليك واصبر حتى يحكم الله وهو خير الحاكمين |
| | | Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci. |
|
1474 | 11 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم الر كتاب أحكمت آياته ثم فصلت من لدن حكيم خبير |
| | | A. L̃.R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa'an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa. |
|
1475 | 11 | 2 | ألا تعبدوا إلا الله إنني لكم منه نذير وبشير |
| | | Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi. |
|
1476 | 11 | 3 | وأن استغفروا ربكم ثم توبوا إليه يمتعكم متاعا حسنا إلى أجل مسمى ويؤت كل ذي فضل فضله وإن تولوا فإني أخاف عليكم عذاب يوم كبير |
| | | Kuma ku nẽmi gãfara gun Ubangijinku. Sa'an nan ku tũba zuwa gare Shi, Ya jiyar da ku dãɗi, jiyarwa mai kyau zuwa ga ajali ambatacce, kuma Ya bai wa dukkan ma'abucin, girma girmansa. Amma idan kun jũya, to, lalle nĩ, inã tsõron azãbar yini mai girma a kanku. |
|
1477 | 11 | 4 | إلى الله مرجعكم وهو على كل شيء قدير |
| | | Zuwa ga Allah makõmarku take, kuma Shĩ a kan kõmeMai ĩkon yi ne. |
|
1478 | 11 | 5 | ألا إنهم يثنون صدورهم ليستخفوا منه ألا حين يستغشون ثيابهم يعلم ما يسرون وما يعلنون إنه عليم بذات الصدور |
| | | To, lalle sũ sunã karkatar da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã. |
|