نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1425 | 10 | 61 | وما تكون في شأن وما تتلو منه من قرآن ولا تعملون من عمل إلا كنا عليكم شهودا إذ تفيضون فيه وما يعزب عن ربك من مثقال ذرة في الأرض ولا في السماء ولا أصغر من ذلك ولا أكبر إلا في كتاب مبين |
| | | Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, fãce Mun kasance Halarce a lõkacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra bã zai yi nĩsa ba daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma bãbu wanda yake mafi ƙaranci daga haka, kuma bãbu mafi girma, fãce yana a cikin littãfi bayyananne. |
|
1426 | 10 | 62 | ألا إن أولياء الله لا خوف عليهم ولا هم يحزنون |
| | | To, Lalle ne masõyan Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bã zã su kasance sunã yin baƙin ciki ba. |
|
1427 | 10 | 63 | الذين آمنوا وكانوا يتقون |
| | | Waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa. |
|
1428 | 10 | 64 | لهم البشرى في الحياة الدنيا وفي الآخرة لا تبديل لكلمات الله ذلك هو الفوز العظيم |
| | | Sunã da bushãra a cikin rãyuwar dũniya da ta Lãhira. Bãbu musanyãwa ga kalmõmin Allah. Wancan shi ne babban rabo mai girma, |
|
1429 | 10 | 65 | ولا يحزنك قولهم إن العزة لله جميعا هو السميع العليم |
| | | Kada maganarsu ta sanya ka a cikin baƙin ciki. Lalle ne alfarma ga Allah take gaba ɗaya. Shi ne Mai jĩ, Masani. |
|
1430 | 10 | 66 | ألا إن لله من في السماوات ومن في الأرض وما يتبع الذين يدعون من دون الله شركاء إن يتبعون إلا الظن وإن هم إلا يخرصون |
| | | To! Haƙĩƙa Allah Yanã da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, bã su biyar waɗansu abõkan tarẽwa (ga Allah a MulkinSa). Bã su biyar kõme fãce zato. Kuma ba su zama ba fãce sunã ƙiri faɗi kawai. |
|
1431 | 10 | 67 | هو الذي جعل لكم الليل لتسكنوا فيه والنهار مبصرا إن في ذلك لآيات لقوم يسمعون |
| | | Shĩ ne wanda Ya sanya muku dare, dõmin ku natsu a cikinsa, da yini mai sanya a yi gani. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda sukẽ ji. |
|
1432 | 10 | 68 | قالوا اتخذ الله ولدا سبحانه هو الغني له ما في السماوات وما في الأرض إن عندكم من سلطان بهذا أتقولون على الله ما لا تعلمون |
| | | Suka ce: "Allah Ya riƙi ɗa." Tsarkinsa yã tabbata! Shi ne wadãtacce Yanã da mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku bãbu wani dalĩli game da wannan! Shin, kunã faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah? |
|
1433 | 10 | 69 | قل إن الذين يفترون على الله الكذب لا يفلحون |
| | | Ka ce: "Haƙĩƙa waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, bã zã su ci nasara ba." |
|
1434 | 10 | 70 | متاع في الدنيا ثم إلينا مرجعهم ثم نذيقهم العذاب الشديد بما كانوا يكفرون |
| | | Jin dãɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makõmarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azãba mai tsanani sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci. |
|