نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1354 | 9 | 119 | يا أيها الذين آمنوا اتقوا الله وكونوا مع الصادقين |
| | | Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku kasance tãre da mãsu gaskiya. |
|
1355 | 9 | 120 | ما كان لأهل المدينة ومن حولهم من الأعراب أن يتخلفوا عن رسول الله ولا يرغبوا بأنفسهم عن نفسه ذلك بأنهم لا يصيبهم ظمأ ولا نصب ولا مخمصة في سبيل الله ولا يطئون موطئا يغيظ الكفار ولا ينالون من عدو نيلا إلا كتب لهم به عمل صالح إن الله لا يضيع أجر المحسنين |
| | | Bã ya kasancẽwa ga mutãnen Madĩna da wanda yake a gẽfensu, daga ƙauyãwã, su sãba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rãyukansu daga ransa. Wancan, sabõda ƙishirwa bã ta sãmun su, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyai Allah, kuma bã su tãkin wani matãki wanda yake takaitar da kãfirai kuma bã su sãmun wani sãmu daga maƙiyi fãce an rubuta musu da shi, lãdar aiki na ƙwarai. Lallai ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa. |
|
1356 | 9 | 121 | ولا ينفقون نفقة صغيرة ولا كبيرة ولا يقطعون واديا إلا كتب لهم ليجزيهم الله أحسن ما كانوا يعملون |
| | | Kuma bã su ciyar da wata ciyarwa, ƙarama kõ babba, kuma bã su kẽta wani rafi sai an rubutã musu, dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyãwon abin da suka kasance sunã aikatãwa. |
|
1357 | 9 | 122 | وما كان المؤمنون لينفروا كافة فلولا نفر من كل فرقة منهم طائفة ليتفقهوا في الدين ولينذروا قومهم إذا رجعوا إليهم لعلهم يحذرون |
| | | Kuma bã ya kasancẽwã ga muminai su fita zuwa yãƙi gabã ɗaya. Sabõda haka, don me ne wata jama'a daga kowane ɓangare daga gare su ba ta fita (zuwa nẽman ilimi ba) dõmin su nẽmi ilimi ga fahimtar addĩni kuma dõmin su yi gargaɗi ga mutãnensu idan sun kõma zuwa gare su, tsammãninsu, sunã yin sauna? |
|
1358 | 9 | 123 | يا أيها الذين آمنوا قاتلوا الذين يلونكم من الكفار وليجدوا فيكم غلظة واعلموا أن الله مع المتقين |
| | | Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yãƙi waɗanda suke kusantar ku daga kãfirai. Kuma su sami tsanani daga gare ku. Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa. |
|
1359 | 9 | 124 | وإذا ما أنزلت سورة فمنهم من يقول أيكم زادته هذه إيمانا فأما الذين آمنوا فزادتهم إيمانا وهم يستبشرون |
| | | Kuma idan aka saukar da wata sũra, to, daga gare su akwai waɗanda suke cẽwa: "Wãne a cikinku wannan sũra ta ƙãra masa ĩmãni?" To amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sũ, sunã yin bushãra (da ita). |
|
1360 | 9 | 125 | وأما الذين في قلوبهم مرض فزادتهم رجسا إلى رجسهم وماتوا وهم كافرون |
| | | Amma kuma waɗanda suke a cikin zukãtansu akwai cũta, to, tã ƙãra musu ƙazanta zuwa ga ƙazantarsu, kuma su mutu alhãlin kuwa sunã kãfirai. |
|
1361 | 9 | 126 | أولا يرون أنهم يفتنون في كل عام مرة أو مرتين ثم لا يتوبون ولا هم يذكرون |
| | | Shin, bã su ganin cẽwa anã fitinar su a cikin kõwace shẽkara: Sau ɗaya kõ kuwa sau biyu, sa'an nan kuma bã su tũba, kuma ba su zama sunã tunãni ba? |
|
1362 | 9 | 127 | وإذا ما أنزلت سورة نظر بعضهم إلى بعض هل يراكم من أحد ثم انصرفوا صرف الله قلوبهم بأنهم قوم لا يفقهون |
| | | "Kuma idan haƙĩƙa, aka saukar da wata sũra, sai sãshensu ya yi dũbi zuwa ga wani sãshe, (su ce): "Shin, wani mutum yanã ganin ku?" Sa'an nan kuma sai su jũya. Allah Ya jũyar da zukãtansu, dõmin, haƙĩƙa sũ mutãne ne, bã su fahimta. |
|
1363 | 9 | 128 | لقد جاءكم رسول من أنفسكم عزيز عليه ما عنتم حريص عليكم بالمؤمنين رءوف رحيم |
| | | Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai. |
|