نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1345 | 9 | 110 | لا يزال بنيانهم الذي بنوا ريبة في قلوبهم إلا أن تقطع قلوبهم والله عليم حكيم |
| | | Gininsu, wanda suka gina, bã zai gushe ba Yanã abin shakka a cikin zukãtansu fãce idan zukãtansu sun yanyanke. Kuma Allah ne Masani, Mai Hikima. |
|
1346 | 9 | 111 | إن الله اشترى من المؤمنين أنفسهم وأموالهم بأن لهم الجنة يقاتلون في سبيل الله فيقتلون ويقتلون وعدا عليه حقا في التوراة والإنجيل والقرآن ومن أوفى بعهده من الله فاستبشروا ببيعكم الذي بايعتم به وذلك هو الفوز العظيم |
| | | Lalle ne, Allah Ya saya daga mummunai, rãyukansu da dũkiyõyinsu, da cẽwa sunã da Aljanna, sunã yin yãƙi a cikin hanyar Allah, sabõda haka sunã kashẽwa anã kashẽ su. (Allah Yã yi) wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjĩla da Alƙur'ãni. Kuma wãne ne mafi cikãwa da alkawarinsa daga Allah? Sabõda haka ku yi bushãra da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo, mai girma. |
|
1347 | 9 | 112 | التائبون العابدون الحامدون السائحون الراكعون الساجدون الآمرون بالمعروف والناهون عن المنكر والحافظون لحدود الله وبشر المؤمنين |
| | | Mãsu tũba, mãsu bautãwa, mãsu gõdẽwa, mãsu tafiya, mãsu ruku'i, mãsu sujada mãsu umurni da alhẽri da mãsu hani daga abin da aka ƙi da mãsu tsarẽwaã ga iyãkõkin Allah. Kuma ka bãyar da bushãra ga muminai. |
|
1348 | 9 | 113 | ما كان للنبي والذين آمنوا أن يستغفروا للمشركين ولو كانوا أولي قربى من بعد ما تبين لهم أنهم أصحاب الجحيم |
| | | Bã ya kasancẽwa ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne. |
|
1349 | 9 | 114 | وما كان استغفار إبراهيم لأبيه إلا عن موعدة وعدها إياه فلما تبين له أنه عدو لله تبرأ منه إن إبراهيم لأواه حليم |
| | | Kuma istigifãrin Ibrãhĩm ga ubansa bai kasance ba fãce sabõda wani wa'adi ne da ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lõkacin da ya bayyana a gare shi (Ibrãhĩm) cẽwa lalle ne shĩ (ubansa) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙĩƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri. |
|
1350 | 9 | 115 | وما كان الله ليضل قوما بعد إذ هداهم حتى يبين لهم ما يتقون إن الله بكل شيء عليم |
| | | Kuma Allah bai kasance mai ɓatar da mutãne a bãyan Yã shiryar da su ba, sai Ya bayyanã musu abin da zã su yi taƙawa da shi. Lalle ne Alllh, ga kõme, Masani ne. |
|
1351 | 9 | 116 | إن الله له ملك السماوات والأرض يحيي ويميت وما لكم من دون الله من ولي ولا نصير |
| | | Lalle ne Allah Yanã da mulkin sammai da ƙasa, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa. Kuma bã ku da wani masõyi, kuma bã ku da mataimaki, baicin Allah. |
|
1352 | 9 | 117 | لقد تاب الله على النبي والمهاجرين والأنصار الذين اتبعوه في ساعة العسرة من بعد ما كاد يزيغ قلوب فريق منهم ثم تاب عليهم إنه بهم رءوف رحيم |
| | | Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Ya karɓi tũbar Anbabi da Muhãjirĩna da Ansãr waɗanda suka bĩ shi, a cikin sã'ar tsanani, daga bãya zukãtan wani ɓangare daga gare su sun yi kusa su karkata, sa'an nan (Allah) Ya karɓi tũbarsu. Lalle, Shĩ ne Mai tausayi, Mai jin ƙai gare su. |
|
1353 | 9 | 118 | وعلى الثلاثة الذين خلفوا حتى إذا ضاقت عليهم الأرض بما رحبت وضاقت عليهم أنفسهم وظنوا أن لا ملجأ من الله إلا إليه ثم تاب عليهم ليتوبوا إن الله هو التواب الرحيم |
| | | Kuma (Allah) Yã karɓi tũba a kan ukun nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rãyukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton bãbu wata mafakã daga Allah fãce (kõmãwa) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tũbarsu, dõmin su tabbata a kan tũba. Lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai. |
|
1354 | 9 | 119 | يا أيها الذين آمنوا اتقوا الله وكونوا مع الصادقين |
| | | Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku kasance tãre da mãsu gaskiya. |
|