نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1297 | 9 | 62 | يحلفون بالله لكم ليرضوكم والله ورسوله أحق أن يرضوه إن كانوا مؤمنين |
| | | Sunã rantsuwa da Allah sabõda ku, dõmin su yardar da ku. Kuma Allah da ManzonSa ne mafi cancantar su yardar da Shi, idan sun kasance mũminai. |
|
1298 | 9 | 63 | ألم يعلموا أنه من يحادد الله ورسوله فأن له نار جهنم خالدا فيها ذلك الخزي العظيم |
| | | Shin, ba su sani ba cẽwa "Lalle ne wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, haƙĩƙa Yanã da wutar Jahannama, Yanã madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulãkantãwa babba!" |
|
1299 | 9 | 64 | يحذر المنافقون أن تنزل عليهم سورة تنبئهم بما في قلوبهم قل استهزئوا إن الله مخرج ما تحذرون |
| | | Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu, wadda take bã su lãbãri ga abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: "Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai da abin da kuke tsõro." |
|
1300 | 9 | 65 | ولئن سألتهم ليقولن إنما كنا نخوض ونلعب قل أبالله وآياته ورسوله كنتم تستهزئون |
| | | Kuma lalle ne, idan ka tambaye, su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?" |
|
1301 | 9 | 66 | لا تعتذروا قد كفرتم بعد إيمانكم إن نعف عن طائفة منكم نعذب طائفة بأنهم كانوا مجرمين |
| | | "Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyanĩmãninku. Idan Mun yãfe laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, zã Mu azabta wata ƙungiya sabõda, lalle, sun kasance mãsu laifi." |
|
1302 | 9 | 67 | المنافقون والمنافقات بعضهم من بعض يأمرون بالمنكر وينهون عن المعروف ويقبضون أيديهم نسوا الله فنسيهم إن المنافقين هم الفاسقون |
| | | Munãfukai maza da munãfukai mãtã, sãshensu daga sãshe, sunã umurni da abin ƙi kuma sunã hani daga alhẽri. Kuma sunã damƙẽwar hannayensu. Sun mance Allah, sai Ya mantã da su. Lalle ne munãfukai sũ ne fãsiƙai. |
|
1303 | 9 | 68 | وعد الله المنافقين والمنافقات والكفار نار جهنم خالدين فيها هي حسبهم ولعنهم الله ولهم عذاب مقيم |
| | | Allah yã yi wa'adi ga munãfukai maza da munãfukai mãtã da kãfirai da wutar Jahannama, sunã madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Yã la'ance su, kuma sunã da azãba zaunanniya. |
|
1304 | 9 | 69 | كالذين من قبلكم كانوا أشد منكم قوة وأكثر أموالا وأولادا فاستمتعوا بخلاقهم فاستمتعتم بخلاقكم كما استمتع الذين من قبلكم بخلاقهم وخضتم كالذي خاضوا أولئك حبطت أعمالهم في الدنيا والآخرة وأولئك هم الخاسرون |
| | | Kamar waɗanda suke a gabãninku, sun kasance mafi tsananin ƙarfi daga gare ku, kuma mafi yawan dũkiyõyi da ɗiya. Sai suka ji daɗi da rabonsu, sai kuka ji daɗi da rabonku kamar yadda waɗanda suke a gabãninku suka ji dãɗi, da rabonsu, kuma kuka kũtsa kamar kũtsãwarsu. Waɗancan ayyukansu sun ɓãci a dũniya da Lãhira, kuma waɗannan sũ ne mãsu hasãra. |
|
1305 | 9 | 70 | ألم يأتهم نبأ الذين من قبلهم قوم نوح وعاد وثمود وقوم إبراهيم وأصحاب مدين والمؤتفكات أتتهم رسلهم بالبينات فما كان الله ليظلمهم ولكن كانوا أنفسهم يظلمون |
| | | Shin lãbarin waɗanda suke a gabãninsu bai je musu ba, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da mutãnen Ibrãhĩm da Ma'abũta Madyana da waɗanda aka birkice? Manzanninsu sun jẽ musu da ãyõyayi bayanannu. To, Allah bai kasance Yanã zãluntar su ba, amma sun kasance rãyukansu suke zãlunta. |
|
1306 | 9 | 71 | والمؤمنون والمؤمنات بعضهم أولياء بعض يأمرون بالمعروف وينهون عن المنكر ويقيمون الصلاة ويؤتون الزكاة ويطيعون الله ورسوله أولئك سيرحمهم الله إن الله عزيز حكيم |
| | | Kuma mummunai maza da mummunai mãtã sãshensu majiɓincin sãshe ne, sunã umurni da alhẽri kuma sunã hani daga abin da bã a so, kuma sunã tsayar da salla, kuma sunã bãyar da zakka, kuma sunãɗã'a ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima. |
|