نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1222 | 8 | 62 | وإن يريدوا أن يخدعوك فإن حسبك الله هو الذي أيدك بنصره وبالمؤمنين |
| | | Kuma idan sun yi nufin su yaudare ka, to, lalle ma'ishinka Allah ne, Shĩ ne wanda Ya ƙarfafa ka da taimakonSa, kuma da mũminai. |
|
1223 | 8 | 63 | وألف بين قلوبهم لو أنفقت ما في الأرض جميعا ما ألفت بين قلوبهم ولكن الله ألف بينهم إنه عزيز حكيم |
| | | Kuma Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu. Dã kã ciyar da abin da yake cikin ƙasa, gabã ɗaya, dã ba ka sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu ba, kuma amma Allah Yã sanya sõyayya a tsakãninsu. Lalle Shi ne Mabuwãyi, Mai hikima. |
|
1224 | 8 | 64 | يا أيها النبي حسبك الله ومن اتبعك من المؤمنين |
| | | Ya kai Annabi! Ma'ishinka Allah ne, kai da wanda ya biye maka daga mũminai. |
|
1225 | 8 | 65 | يا أيها النبي حرض المؤمنين على القتال إن يكن منكم عشرون صابرون يغلبوا مائتين وإن يكن منكم مائة يغلبوا ألفا من الذين كفروا بأنهم قوم لا يفقهون |
| | | Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da mũminai a kan yãƙi. Idan mutum ashirin mãsu haƙuri sun kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan kuma idan ɗari suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu daga waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ, mutãne ne bã su fahimta. |
|
1226 | 8 | 66 | الآن خفف الله عنكم وعلم أن فيكم ضعفا فإن يكن منكم مائة صابرة يغلبوا مائتين وإن يكن منكم ألف يغلبوا ألفين بإذن الله والله مع الصابرين |
| | | A yanzu Allah Yã sauƙaƙe daga gare ku, kuma Yã sani cẽwa lalle ne akwai mãsu rauni a cikinku. To, idan mutum ɗari, mãsu haƙuri, suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu biyu, da iznin Allah. Kuma Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri. |
|
1227 | 8 | 67 | ما كان لنبي أن يكون له أسرى حتى يثخن في الأرض تريدون عرض الدنيا والله يريد الآخرة والله عزيز حكيم |
| | | Bã ya kasancewa ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima. |
|
1228 | 8 | 68 | لولا كتاب من الله سبق لمسكم فيما أخذتم عذاب عظيم |
| | | Bã dõmin wani Littãfi daga Allah ba, wanda ya gabãta, dã azãba mai girma daga Allah tã shãfe ku a cikin abin da kuka kãma. |
|
1229 | 8 | 69 | فكلوا مما غنمتم حلالا طيبا واتقوا الله إن الله غفور رحيم |
| | | Sabõda haka, ku ci daga abin da kuka sãmu ganĩma, Yanã halal mai kyau. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. |
|
1230 | 8 | 70 | يا أيها النبي قل لمن في أيديكم من الأسرى إن يعلم الله في قلوبكم خيرا يؤتكم خيرا مما أخذ منكم ويغفر لكم والله غفور رحيم |
| | | Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: "Idan Allah Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." |
|
1231 | 8 | 71 | وإن يريدوا خيانتك فقد خانوا الله من قبل فأمكن منهم والله عليم حكيم |
| | | Kuma idan sun yi nufin yaudararka, to, haƙĩƙa, sun yaudari Allahdaga gabãni sai Ya bãyar da dãmã daga gare su: Kuma Allah ne Masani, Mai hikima. |
|