نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1206 | 8 | 46 | وأطيعوا الله ورسوله ولا تنازعوا فتفشلوا وتذهب ريحكم واصبروا إن الله مع الصابرين |
| | | Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jãyayya har ku raunana kuma iskarku ta tafi, kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri. |
|
1207 | 8 | 47 | ولا تكونوا كالذين خرجوا من ديارهم بطرا ورئاء الناس ويصدون عن سبيل الله والله بما يعملون محيط |
| | | Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu, sunã mãsu alfahari da yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa. |
|
1208 | 8 | 48 | وإذ زين لهم الشيطان أعمالهم وقال لا غالب لكم اليوم من الناس وإني جار لكم فلما تراءت الفئتان نكص على عقبيه وقال إني بريء منكم إني أرى ما لا ترون إني أخاف الله والله شديد العقاب |
| | | Kuma a lõkacin da Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: "Bãbu marinjayi a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku." To, a lõkacin da ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: "Lalle ne nĩ barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne." |
|
1209 | 8 | 49 | إذ يقول المنافقون والذين في قلوبهم مرض غر هؤلاء دينهم ومن يتوكل على الله فإن الله عزيز حكيم |
| | | A lõkacin da munãfukai da waɗanda suke akwai cũtã a cikin zukãtansu, suke cẽwa: "Addĩnin waɗannan yã rũɗe su" Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima. |
|
1210 | 8 | 50 | ولو ترى إذ يتوفى الذين كفروا الملائكة يضربون وجوههم وأدبارهم وذوقوا عذاب الحريق |
| | | Kuma dã kã gani, a lõkacin da Malã'iku suke karɓar rãyukan waɗanda suka kãfirta, sunã dukar fuskõkinsu da ɗuwãwunsu, kuma suna cẽwa: "Ku ɗanɗani azãbar Gõbara." |
|
1211 | 8 | 51 | ذلك بما قدمت أيديكم وأن الله ليس بظلام للعبيد |
| | | "Wancan sabõda abin da hannãyenku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne, Allah bai zama Mai zãlunci ba ga, bãyinSa." |
|
1212 | 8 | 52 | كدأب آل فرعون والذين من قبلهم كفروا بآيات الله فأخذهم الله بذنوبهم إن الله قوي شديد العقاب |
| | | "Kamar al'ãdar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke gabãninsu, sun kãfirta da ãyõyin Allah, sai Allah Ya kãma su da zunubansu. Lalle Allah ne Mai ƙarfi, Mai tsananin uƙũba. |
|
1213 | 8 | 53 | ذلك بأن الله لم يك مغيرا نعمة أنعمها على قوم حتى يغيروا ما بأنفسهم وأن الله سميع عليم |
| | | "Wancan ne, dõmin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni'ima wadda ya ni'imtar da ita a kan wasu mutãne ba fãce sun sãke abin da yake ga rãyukansu, kuma dõmin lalle Allah ne Mai jĩ, Masani." |
|
1214 | 8 | 54 | كدأب آل فرعون والذين من قبلهم كذبوا بآيات ربهم فأهلكناهم بذنوبهم وأغرقنا آل فرعون وكل كانوا ظالمين |
| | | Kamar al'adar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata game da ãyõyin Ubangijinsu, sai Muka halaka su, sabõda zunubansu, kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna. Kuma dukansu sun kasance ne mãsu zãlunci. |
|
1215 | 8 | 55 | إن شر الدواب عند الله الذين كفروا فهم لا يؤمنون |
| | | Lalle mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne waɗanda suka kãfirta, sa'an nan bã zã su yi ĩmãni ba. |
|