نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1196 | 8 | 36 | إن الذين كفروا ينفقون أموالهم ليصدوا عن سبيل الله فسينفقونها ثم تكون عليهم حسرة ثم يغلبون والذين كفروا إلى جهنم يحشرون |
| | | Lalle ne waɗanda suka kãfirta, sunã ciyar da dũkiyõyinsu, dõmin su kange daga hanyar Allah; to, zã a su ciyar da ita, sa' an nan kuma ta kasance nadãma a kansu, sa'an nan kuma a rinjãye su. Kuma waɗanda suka kãfirta zuwa ga Jahannama ake tãra su; |
|
1197 | 8 | 37 | ليميز الله الخبيث من الطيب ويجعل الخبيث بعضه على بعض فيركمه جميعا فيجعله في جهنم أولئك هم الخاسرون |
| | | Dõmin Allah Ya rarrabe mummũna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummũnan, sãshensa a kan sãshe, sa'an nan Ya shirga shi gabã daya, sa'an nan Ya sanyã shi a cikin Jahannama. Waɗannan sũ ne mãsu hasãra. |
|
1198 | 8 | 38 | قل للذين كفروا إن ينتهوا يغفر لهم ما قد سلف وإن يعودوا فقد مضت سنت الأولين |
| | | Ka ce wa waɗanda suka kãfirta, idan sun hanu, zã a gãfarta musu abin da ya riga ya shige, kuma idan sun kõma, to, hanyar kãfiran farko, haƙĩƙa, ta shũɗe. |
|
1199 | 8 | 39 | وقاتلوهم حتى لا تكون فتنة ويكون الدين كله لله فإن انتهوا فإن الله بما يعملون بصير |
| | | Kuma ku yãƙe su har wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini dukansa ya kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatãwa Mai gani ne. |
|
1200 | 8 | 40 | وإن تولوا فاعلموا أن الله مولاكم نعم المولى ونعم النصير |
| | | Kuma idan sun jũya, to, ku sani cẽwa lalle Allah ne Majiɓincinku: Mãdalla da Majiɓinci, kuma mãdalla da Mai taimako, Shĩ. |
|
1201 | 8 | 41 | واعلموا أنما غنمتم من شيء فأن لله خمسه وللرسول ولذي القربى واليتامى والمساكين وابن السبيل إن كنتم آمنتم بالله وما أنزلنا على عبدنا يوم الفرقان يوم التقى الجمعان والله على كل شيء قدير |
| | | Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi ganĩma daga wani abu, to, lalle ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama'a biyu suka haɗu, kuma Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi. |
|
1202 | 8 | 42 | إذ أنتم بالعدوة الدنيا وهم بالعدوة القصوى والركب أسفل منكم ولو تواعدتم لاختلفتم في الميعاد ولكن ليقضي الله أمرا كان مفعولا ليهلك من هلك عن بينة ويحيى من حي عن بينة وإن الله لسميع عليم |
| | | A lõkacin da kuke a gãɓa ta kusa sũ kuma sunã a gãɓa tanẽsa, kuma ãyarin yana a wuri mafi gangarãwa daga gare ku, kuma dã kun yi wa jũna wa'adi, dã kun sãɓa ga wa'adin; kuma amma dõmin Allah Ya hukunta abin da yake ya kasance abin aikatãwa. Dõmin wanda yake halaka ya halaka daga shaida, kuma mai rãyuwa ya rãyu daga shaida, kuma lalle Allah ne, haƙĩƙa, Mai ji Masani. |
|
1203 | 8 | 43 | إذ يريكهم الله في منامك قليلا ولو أراكهم كثيرا لفشلتم ولتنازعتم في الأمر ولكن الله سلم إنه عليم بذات الصدور |
| | | A lõkacin da Allah Yake nũna maka sũ sunã kaɗan, a cikin barcinka, kuma dã Ya nũna maka su sunã da, yawa, lalle ne dã kun ji tsõro, kuma lalle ne dã kun yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma amma Allah Yã tsare ku: Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake a cikin ƙirãza. |
|
1204 | 8 | 44 | وإذ يريكموهم إذ التقيتم في أعينكم قليلا ويقللكم في أعينهم ليقضي الله أمرا كان مفعولا وإلى الله ترجع الأمور |
| | | Kuma a lõkacin da Yake nũna muku su, a lõkacin da kuka haɗu, a cikin idanunku sunã kaɗan, kuma Ya ƙarantar da ku a cikin idanunsu dõmin Allah Ya hukunta wani al'amari wanda ya kasance abin aikatãwa. Kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'umurra. |
|
1205 | 8 | 45 | يا أيها الذين آمنوا إذا لقيتم فئة فاثبتوا واذكروا الله كثيرا لعلكم تفلحون |
| | | Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku tabbata, kuma ku ambaci Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara. |
|