نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1159 | 7 | 205 | واذكر ربك في نفسك تضرعا وخيفة ودون الجهر من القول بالغدو والآصال ولا تكن من الغافلين |
| | | Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu. |
|
1160 | 7 | 206 | إن الذين عند ربك لا يستكبرون عن عبادته ويسبحونه وله يسجدون |
| | | Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada. |
|
1161 | 8 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم يسألونك عن الأنفال قل الأنفال لله والرسول فاتقوا الله وأصلحوا ذات بينكم وأطيعوا الله ورسوله إن كنتم مؤمنين |
| | | Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai." |
|
1162 | 8 | 2 | إنما المؤمنون الذين إذا ذكر الله وجلت قلوبهم وإذا تليت عليهم آياته زادتهم إيمانا وعلى ربهم يتوكلون |
| | | Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara. |
|
1163 | 8 | 3 | الذين يقيمون الصلاة ومما رزقناهم ينفقون |
| | | Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa. |
|
1164 | 8 | 4 | أولئك هم المؤمنون حقا لهم درجات عند ربهم ومغفرة ورزق كريم |
| | | Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci. |
|
1165 | 8 | 5 | كما أخرجك ربك من بيتك بالحق وإن فريقا من المؤمنين لكارهون |
| | | Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma. |
|
1166 | 8 | 6 | يجادلونك في الحق بعدما تبين كأنما يساقون إلى الموت وهم ينظرون |
| | | Sunã jãyayya da kai a cikin (sha'anin) gaskiya a bãyan tã bayYanã, kamar dai lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo. |
|
1167 | 8 | 7 | وإذ يعدكم الله إحدى الطائفتين أنها لكم وتودون أن غير ذات الشوكة تكون لكم ويريد الله أن يحق الحق بكلماته ويقطع دابر الكافرين |
| | | Kuma a lõkacin da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai; |
|
1168 | 8 | 8 | ليحق الحق ويبطل الباطل ولو كره المجرمون |
| | | Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi. |
|