نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1152 | 7 | 198 | وإن تدعوهم إلى الهدى لا يسمعوا وتراهم ينظرون إليك وهم لا يبصرون |
| | | Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani. |
|
1153 | 7 | 199 | خذ العفو وأمر بالعرف وأعرض عن الجاهلين |
| | | Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai. |
|
1154 | 7 | 200 | وإما ينزغنك من الشيطان نزغ فاستعذ بالله إنه سميع عليم |
| | | Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani. |
|
1155 | 7 | 201 | إن الذين اتقوا إذا مسهم طائف من الشيطان تذكروا فإذا هم مبصرون |
| | | Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basĩra. |
|
1156 | 7 | 202 | وإخوانهم يمدونهم في الغي ثم لا يقصرون |
| | | Kuma 'yan'uwan su (shaiɗanu) sunã taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma bã su taƙaitãwa. |
|
1157 | 7 | 203 | وإذا لم تأتهم بآية قالوا لولا اجتبيتها قل إنما أتبع ما يوحى إلي من ربي هذا بصائر من ربكم وهدى ورحمة لقوم يؤمنون |
| | | Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: "Don me ba ka ƙãga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin imãni." |
|
1158 | 7 | 204 | وإذا قرئ القرآن فاستمعوا له وأنصتوا لعلكم ترحمون |
| | | Kuma idan an karanta Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama. |
|
1159 | 7 | 205 | واذكر ربك في نفسك تضرعا وخيفة ودون الجهر من القول بالغدو والآصال ولا تكن من الغافلين |
| | | Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu. |
|
1160 | 7 | 206 | إن الذين عند ربك لا يستكبرون عن عبادته ويسبحونه وله يسجدون |
| | | Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada. |
|
1161 | 8 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم يسألونك عن الأنفال قل الأنفال لله والرسول فاتقوا الله وأصلحوا ذات بينكم وأطيعوا الله ورسوله إن كنتم مؤمنين |
| | | Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai." |
|