نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1142 | 7 | 188 | قل لا أملك لنفسي نفعا ولا ضرا إلا ما شاء الله ولو كنت أعلم الغيب لاستكثرت من الخير وما مسني السوء إن أنا إلا نذير وبشير لقوم يؤمنون |
| | | Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni." |
|
1143 | 7 | 189 | هو الذي خلقكم من نفس واحدة وجعل منها زوجها ليسكن إليها فلما تغشاها حملت حملا خفيفا فمرت به فلما أثقلت دعوا الله ربهما لئن آتيتنا صالحا لنكونن من الشاكرين |
| | | Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare ta, ma'auranta, dõmin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa'an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõƙi Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka bã mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, zã mu kasance dagamãsu gõdiya." |
|
1144 | 7 | 190 | فلما آتاهما صالحا جعلا له شركاء فيما آتاهما فتعالى الله عما يشركون |
| | | To, a lõkacin da Ya bã su abin ƙwarai, suka sanya Masa abõkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yã tsarkaka daga abin da suke yi na shirki. |
|
1145 | 7 | 191 | أيشركون ما لا يخلق شيئا وهم يخلقون |
| | | Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa? |
|
1146 | 7 | 192 | ولا يستطيعون لهم نصرا ولا أنفسهم ينصرون |
| | | Kuma ba su iya bãyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bã su iya taimaka! |
|
1147 | 7 | 193 | وإن تدعوهم إلى الهدى لا يتبعوكم سواء عليكم أدعوتموهم أم أنتم صامتون |
| | | Kuma idan kun kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirãye su, kõ kuwa kũ mãsu kawaici ne! |
|
1148 | 7 | 194 | إن الذين تدعون من دون الله عباد أمثالكم فادعوهم فليستجيبوا لكم إن كنتم صادقين |
| | | Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance mãsu gaskiya! |
|
1149 | 7 | 195 | ألهم أرجل يمشون بها أم لهم أيد يبطشون بها أم لهم أعين يبصرون بها أم لهم آذان يسمعون بها قل ادعوا شركاءكم ثم كيدون فلا تنظرون |
| | | Shin sunã da ƙafãfu da suke yin tafia da su? Kõ sunã da hannãye da suke damƙa da su? Kõ sunã da idãnu da suke gani da su? Ko sunã da kunnuwa da suke saurãre da su? Ka ce: "Ku kirãwo abũbuwan shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurãra mini." |
|
1150 | 7 | 196 | إن وليي الله الذي نزل الكتاب وهو يتولى الصالحين |
| | | "Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sãlihai," |
|
1151 | 7 | 197 | والذين تدعون من دونه لا يستطيعون نصركم ولا أنفسهم ينصرون |
| | | "Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka." |
|