نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1101 | 7 | 147 | والذين كذبوا بآياتنا ولقاء الآخرة حبطت أعمالهم هل يجزون إلا ما كانوا يعملون |
| | | Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa? |
|
1102 | 7 | 148 | واتخذ قوم موسى من بعده من حليهم عجلا جسدا له خوار ألم يروا أنه لا يكلمهم ولا يهديهم سبيلا اتخذوه وكانوا ظالمين |
| | | Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci. |
|
1103 | 7 | 149 | ولما سقط في أيديهم ورأوا أنهم قد ضلوا قالوا لئن لم يرحمنا ربنا ويغفر لنا لنكونن من الخاسرين |
| | | Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancẽwa daga mãsu hasãra." |
|
1104 | 7 | 150 | ولما رجع موسى إلى قومه غضبان أسفا قال بئسما خلفتموني من بعدي أعجلتم أمر ربكم وألقى الألواح وأخذ برأس أخيه يجره إليه قال ابن أم إن القوم استضعفوني وكادوا يقتلونني فلا تشمت بي الأعداء ولا تجعلني مع القوم الظالمين |
| | | Kuma a lõkacin da Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa, yanã mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Tir da abin da kuka yi mini wakilci, a bãyanã! Shin, kun nẽmi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan'uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: "Yã ɗan'uwata! Lalle ne mutãnen, sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, sabõda haka kada ka dãrantar da maƙiya game da ni, kuma kada ka sanya ni tãre da mutãne azzãlumai." |
|
1105 | 7 | 151 | قال رب اغفر لي ولأخي وأدخلنا في رحمتك وأنت أرحم الراحمين |
| | | Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka gãfarta mini, nĩ da ɗan'uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarKa, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama!" |
|
1106 | 7 | 152 | إن الذين اتخذوا العجل سينالهم غضب من ربهم وذلة في الحياة الدنيا وكذلك نجزي المفترين |
| | | Lalle ne waɗanda suka riƙi maraƙin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walãkanci a cikin rãyuwar dũniya, zã su sãme su: Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu ƙirƙira ƙarya. |
|
1107 | 7 | 153 | والذين عملوا السيئات ثم تابوا من بعدها وآمنوا إن ربك من بعدها لغفور رحيم |
| | | Kuma waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka, sa'an nan suka tũba daga bãyansu kuma sukayi ĩmãni, lalle ne Ubangijinka daga bãyansu, haƙĩƙa, Mai gãfarane, Mai jin ƙai. |
|
1108 | 7 | 154 | ولما سكت عن موسى الغضب أخذ الألواح وفي نسختها هدى ورحمة للذين هم لربهم يرهبون |
| | | Kuma a lõkacin da fushin ya kwanta daga barin Mũsã, sai ya riƙi Allunan, kuma a cikin kwafensu akwai shiriya da rahama ga waɗanda suke sũ, ga Ubangijinsu, mãsu jin tsõro ne. |
|
1109 | 7 | 155 | واختار موسى قومه سبعين رجلا لميقاتنا فلما أخذتهم الرجفة قال رب لو شئت أهلكتهم من قبل وإياي أتهلكنا بما فعل السفهاء منا إن هي إلا فتنتك تضل بها من تشاء وتهدي من تشاء أنت ولينا فاغفر لنا وارحمنا وأنت خير الغافرين |
| | | Kuma Mũsã ya zãɓi mutãnensa, namiji saba'in dõmin miƙãtinMu. To, a lõkacin da tsãwa ta kãma su, ya ce: "Yã Ubangijina! Dã Kã so, dã Kã halakar da su daga gabãni, sũ da ni. Shin zã Kahalaka mu, sabõda abin da wãwãyen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba fãce fitinarKa Kanã ɓatarwa, da ita, wanda Kake so kuma kanã shiryarwa da ita, wanda Kake so; Kai ne Majiɓincinmu. Sai Ka gãfarta mana; kuma Ka yi mana rahama, alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãfara." |
|
1110 | 7 | 156 | واكتب لنا في هذه الدنيا حسنة وفي الآخرة إنا هدنا إليك قال عذابي أصيب به من أشاء ورحمتي وسعت كل شيء فسأكتبها للذين يتقون ويؤتون الزكاة والذين هم بآياتنا يؤمنون |
| | | "Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ, mun tũba zuwa gare Ka." Ya ce: "AzãbaTa Inã sãmu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa'an nan zã Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyinMu mũminai ne." |
|