نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
12 | 2 | 5 | أولئك على هدى من ربهم وأولئك هم المفلحون |
| | | Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara. |
|
13 | 2 | 6 | إن الذين كفروا سواء عليهم أأنذرتهم أم لم تنذرهم لا يؤمنون |
| | | Lalle ne waɗanda suka kãfirta daidai ne a kansu, shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, ba zã su yi ĩmãni ba. |
|
14 | 2 | 7 | ختم الله على قلوبهم وعلى سمعهم وعلى أبصارهم غشاوة ولهم عذاب عظيم |
| | | Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yãna; kuma suna da wata azãba mai girma. |
|
15 | 2 | 8 | ومن الناس من يقول آمنا بالله وباليوم الآخر وما هم بمؤمنين |
| | | Kuma akwai daga mutãne wanda yake cewa: "Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira." Alhãli kuwa su ba muminai ba ne. |
|
16 | 2 | 9 | يخادعون الله والذين آمنوا وما يخدعون إلا أنفسهم وما يشعرون |
| | | Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu, kuma bã su sakankancẽwa! |
|
17 | 2 | 10 | في قلوبهم مرض فزادهم الله مرضا ولهم عذاب أليم بما كانوا يكذبون |
| | | A cikin zukãtansu akwai wata cũta. Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta, kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya. |
|
18 | 2 | 11 | وإذا قيل لهم لا تفسدوا في الأرض قالوا إنما نحن مصلحون |
| | | Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa," sukan ce: "Mũ mãsu kyautatawa kawai ne!" |
|
19 | 2 | 12 | ألا إنهم هم المفسدون ولكن لا يشعرون |
| | | To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna, kuma amma bã su sansancewa. |
|
20 | 2 | 13 | وإذا قيل لهم آمنوا كما آمن الناس قالوا أنؤمن كما آمن السفهاء ألا إنهم هم السفهاء ولكن لا يعلمون |
| | | Kuma idan aka ce musu: "ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni," sukan ce: "Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?" To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma amma bã su sani. |
|
21 | 2 | 14 | وإذا لقوا الذين آمنوا قالوا آمنا وإذا خلوا إلى شياطينهم قالوا إنا معكم إنما نحن مستهزئون |
| | | Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni, sukan ce: "Mun yi ĩmãni. "Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu, sukan ce: "Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne." |
|