نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1094 | 7 | 140 | قال أغير الله أبغيكم إلها وهو فضلكم على العالمين |
| | | Ya ce: "Shin, wanin Allah nike nẽma muku ya zama abin bautãwa, alhãli kuwa Shĩ (Allah) Ya fĩfĩta ku a kan halittu?" |
|
1095 | 7 | 141 | وإذ أنجيناكم من آل فرعون يسومونكم سوء العذاب يقتلون أبناءكم ويستحيون نساءكم وفي ذلكم بلاء من ربكم عظيم |
| | | Kuma a lõkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã tayã muku mugunyar azãba. sunã karkashe ɗiyanku maza, kuma sunã rãyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa daga Ubangijinku, Mai girma. |
|
1096 | 7 | 142 | وواعدنا موسى ثلاثين ليلة وأتممناها بعشر فتم ميقات ربه أربعين ليلة وقال موسى لأخيه هارون اخلفني في قومي وأصلح ولا تتبع سبيل المفسدين |
| | | Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsã da dare talãtin kuma Muka cikã su da gõma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsã ya ce wa ɗan'uwansa, Hãrũna: "Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi." |
|
1097 | 7 | 143 | ولما جاء موسى لميقاتنا وكلمه ربه قال رب أرني أنظر إليك قال لن تراني ولكن انظر إلى الجبل فإن استقر مكانه فسوف تراني فلما تجلى ربه للجبل جعله دكا وخر موسى صعقا فلما أفاق قال سبحانك تبت إليك وأنا أول المؤمنين |
| | | Kuma a lõkacin da Mũsã ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsã ya ce: "Yã Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Bã zã ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, zã ka gan Ni." Sa'an nan a lõkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyã shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsã ya fãɗi sõmamme. To, a lõkacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Nã tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai." |
|
1098 | 7 | 144 | قال يا موسى إني اصطفيتك على الناس برسالاتي وبكلامي فخذ ما آتيتك وكن من الشاكرين |
| | | Ya ce: "Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa. Sabõda haka ka riƙi abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya." |
|
1099 | 7 | 145 | وكتبنا له في الألواح من كل شيء موعظة وتفصيلا لكل شيء فخذها بقوة وأمر قومك يأخذوا بأحسنها سأريكم دار الفاسقين |
| | | Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu; zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai." |
|
1100 | 7 | 146 | سأصرف عن آياتي الذين يتكبرون في الأرض بغير الحق وإن يروا كل آية لا يؤمنوا بها وإن يروا سبيل الرشد لا يتخذوه سبيلا وإن يروا سبيل الغي يتخذوه سبيلا ذلك بأنهم كذبوا بآياتنا وكانوا عنها غافلين |
| | | Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai. |
|
1101 | 7 | 147 | والذين كذبوا بآياتنا ولقاء الآخرة حبطت أعمالهم هل يجزون إلا ما كانوا يعملون |
| | | Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa? |
|
1102 | 7 | 148 | واتخذ قوم موسى من بعده من حليهم عجلا جسدا له خوار ألم يروا أنه لا يكلمهم ولا يهديهم سبيلا اتخذوه وكانوا ظالمين |
| | | Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci. |
|
1103 | 7 | 149 | ولما سقط في أيديهم ورأوا أنهم قد ضلوا قالوا لئن لم يرحمنا ربنا ويغفر لنا لنكونن من الخاسرين |
| | | Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancẽwa daga mãsu hasãra." |
|