نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
1072 | 7 | 118 | فوقع الحق وبطل ما كانوا يعملون |
| | | Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci. |
|
1073 | 7 | 119 | فغلبوا هنالك وانقلبوا صاغرين |
| | | Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu. |
|
1074 | 7 | 120 | وألقي السحرة ساجدين |
| | | Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada. |
|
1075 | 7 | 121 | قالوا آمنا برب العالمين |
| | | Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu." |
|
1076 | 7 | 122 | رب موسى وهارون |
| | | "Ubangijin Mũsã da Harũna." |
|
1077 | 7 | 123 | قال فرعون آمنتم به قبل أن آذن لكم إن هذا لمكر مكرتموه في المدينة لتخرجوا منها أهلها فسوف تعلمون |
| | | Fir'auna ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni da shi a gabãnin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, mãkirci ne kuka mãkirta a cikin birni, dõmin ku fitar da mutãnensa daga gare shi; To, da sannu zã ku sani." |
|
1078 | 7 | 124 | لأقطعن أيديكم وأرجلكم من خلاف ثم لأصلبنكم أجمعين |
| | | "Lalle ne, inã karkãtse hannãyenku da ƙafãfunku daga sãɓãni, sa'an nan kuma, haƙĩƙa, inã tsĩre, ku gabã ɗaya." |
|
1079 | 7 | 125 | قالوا إنا إلى ربنا منقلبون |
| | | Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne." |
|
1080 | 7 | 126 | وما تنقم منا إلا أن آمنا بآيات ربنا لما جاءتنا ربنا أفرغ علينا صبرا وتوفنا مسلمين |
| | | "Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai! " |
|
1081 | 7 | 127 | وقال الملأ من قوم فرعون أتذر موسى وقومه ليفسدوا في الأرض ويذرك وآلهتك قال سنقتل أبناءهم ونستحيي نساءهم وإنا فوقهم قاهرون |
| | | Kuma mashawarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka?" Ya ce: "Zã mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne." |
|